Kasar Mali Za Ta Bude Tattaunawa Da Masu Ikirarin Jihadi

2021-02-21 08:56:47
Kasar Mali Za Ta Bude Tattaunawa Da Masu Ikirarin Jihadi

Gwamnatin rikon kwarya ta Mali ta sanar da cewa za ta bude tattaunawa da kungiyoyin da suke ikirarin jihadi a kasar.

Pira ministan rikon kwarya na kasar ta Mali Moctar Ouane ya sanar a birnin Bamako cewa; Zai yi matukar kokari domin shirya zabe mai inganci a kasar.

Watanni shida da su ka gabata ne dai sojoji su ka kifar da gwamnatin kasar Mali, bayan da kasar ta yi fama da rikice-rikicen siyasa.

Al’ummar kasar sun rika yin Zanga-zangar ganin an kawo karshen gwamnatin shugaba Bubakar Keita, wanda a karshe kuwa sojoji su ka hambar da ita.

Mali tana fama da kungiyoyi masu dauke da makamai tsakanin masu ikirarin jihadi da kuma masu son ballewa domin kafa kasar Azbinawa.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!