‘Yan Wasa Musulmi A Burtaniya Su Kan Fuskanci Matsalar Nuna Musu Banbanci

2021-02-20 19:33:21
 ‘Yan Wasa Musulmi A Burtaniya Su Kan Fuskanci Matsalar Nuna Musu Banbanci

Wasu rahotanni sun yi nuni da cewa, sakamakon binciken da masana suka gudanar wanda ya hada da musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba a kasar Burtaniya, an iya gane cewa ‘yan wasa musulmi sun fi fuskantar matsaloli a cikin harkokinsu na wasa fiye da wadanda ba musulmi ba a kasar.

Wannan bincike ya yi ishara da yadda yadda aka samu korafe-korafe da dama daga wasu daga cikin ‘yan wasa wadanda musulmi, dangane da yadda ake nuna musu banbanci ko kuma cin zarafinsu.

Bisa ga bayanin, an jima ana mika wadannan korafe-korafe a lokuta da dama ga hukumar kula da harkokin wasanni a kasar ta Burtaniya, amma ba tare da an dauki wani mataki wanda zai iya kawo karshen hakan ba baki daya.

Da dama daga cikin ‘yan wasa musulmi suna bayyana cewa sun fi fuskantar irin wannan matsala daga magoya bayan kungiyoyin da suke buga wa wasa.

A daura da hakan kuma mata musulmi da suke yin wasan kwallon kafa sanye da lullubi a kansu suna kokawa da irin matsalolin da suke fuskanta, wanda hakan yasa wasu da dama daga cikinsu a yanzu sun daina wasan kwallon kafa a kasar domin tsira da mutuncinsu.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!