An Sake Bude Wata Tsohuwar Makabartar Musulmi Da Aka Rufe A Afirka Ta Kudu

Mahukunta a kasar Afirka ta kudu sun
bayar da izinin sake bude wata makabarta ta musulmi domin bizne gawawwakinsu,
sakamako karuwar masu mutuwa saboda corona.
Rahotani daga kasar Afirka ta kudu
sun ce, mahukunta a yankin Cape Town tare da kwamitin musulmi na birnin sun
cimma matsaya kan bude wata tsohuwar makabarta ta musulmi da ke birnin, domin
bizne gawawwakin musulmi da suke mutuwa.
Daya daga cikin mambobin kwamitin
musulmi na birnin kuma jami’in kiwon lafiya ya bayyana cewa, an dauki wanann
matakin ne bayan cimma matsaya tsakanin gwamnatin Cape Town da kuma musulmin
yankin, inda malamai daga cikin musulmi suka bayar da bayani kan halascin yin
hakan.
A cikin kowane wata guda, akalla
musulmi 150 ke rasa rayukansu a birnin Cape Town, wanda hakan yasa makabartar
da suke yin amfani da ita a yanzu ta cika, a kan hakan aka bukaci bude tsohuwar
makabartar birnin domin yin amfani da ita.
An fara bizne gawawwakin musulmi ne
a wannan makabarta tun a shekara ta 1868, amma daga bisani mahukuntan kasar da
suka yi mulkin wariyar launin fata suka rufe wannan makabarta, inda tun daga
lokacin fiye da shekaru dari da suka gabata, har yanzu ba a kara bizne wata
gawar musulmi a wurin ba.
Ana bizne gawawwaki ne a kasar
Afirka ta kudu a lokutan aiki, amma an bai wa musulmi damar bizne gawawwakinsu a
duk lokacin da suke bukata, bisa koyarwar addininsu.
015