Najeriya: Buhari Ya Jinjina Wa Chadi Kan Hadin Kai Da Take Bai Wa Najeriya Kan Sha’anin Tsaro

Shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya bayyana jin dadinsa a kan yadda kasar Chadi ta samar da
karin sojoji ga Najeriya a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a Nijeriya.
A cikin wani rahoto da jaridar
Leadeship ta bayar, ta bayyana cewa jami’in yada labarai na shugaban kasa Mr
Femi Adesina ne, ya bayyana haka a takardar sanarwar da ya raba wa manema
labarai, inda ya ce, shugaban kasar ya yi bayanin ne a yayin da Mr Ahmat Oumar Ahmat
wakili na musamman na shugaban kasar Chadi Shugaba Idriss Deby Itno, ya ziyarce shi a gidan gwamnati da ke Abuja.
Shugaba Buhari ya ce, sanin mahimancin hada kai da kasashe makwabta yasa a lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2015, ya fara ziyartar kasashen da ke makwabtaka da Najeriya, domin neman
goyon bayansu a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda.
Buhari ya kuma yi wa kasar
Chadi fatan alhairi a zaben shugaban kasa da suke shirin gudanarwa a watan
Afrilun wannans hekara ta 2021.
Sojojin Kasar Chadi sun taka muhimmiyar rawa wajen fatattakar 'yan ta'adda a yankunan kasar har ma da wasu yankuna a cikin jihar Borno da ke tarayyar Najeriya.
015