Nijar: Hukumar Zabe Ta Sanar Da Cewa Ta Kammala Shirin Gudanar Da Zaben Shugaban Kasar Zagaye Na Biyu
2021-02-20 14:07:50

Hukumar zaben ta “ CENI” ta gabatar da wani taron manema labaru da a ciki ta bayyana shirye-shiryenta na gudanar da zaben na shugaban kasa zagaye na biyu wanda za a yi a gobe Lahadi 21 ga watan nan na Febrairu.
Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta Issaka Souna ya bayyana cewa; Za Mu shirya zabe ne domin kasar Niger, ba domin kalubalantar wani dan takara ba.”
Bugu da
kari,a yayin taron manema labarun na jiya
juma’a, an yi bitar yadda zaben da ya gudan a watan Disamba na shekarar
da ta gabata.
Har ila yau
Issaka Souna ya ce; Tuni an aike da dukkanin kayan aiki na zaben zuwa dukkanin
gundumomi, kuma wakilan ‘ yan takarar biyu suna bin diddigin dukkanin yadda
shirye-shiryen suke gudana.
Za a yi
gogayya ne a zaben zagaye na biyu a gobe idan Allah ya kai mu a tsakanin
Muhammadu Bazum na jam’iyyar PNDS, mai mulki da kuma Muhammadu Usmana na
jam’iyyar RDR ta adawa.
031
Tags:
hukumar zaben ta “ ceni”
ta bayyana shirye-shiryenta
na gudanar da zaben na shugaban kasa
zagaye na biyu wanda za a yi a gobe lahadi 21
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!