Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Sayi Allurar Rigakafin Covid-19 Miliyan 300 Daga Kasar Rasha

A wata sanarwa da kungiyar ta tarayyar Afirka ta fitar a jiya Juma’a, ta bayyana cewa; Allurar rigakafin ta Sputnik kirar kasar Rasha da ta saya, za ta shiga hannu ne a cikin watanni 12, za kuma a fara kawo ta ne daga watan Mayu na wannan shekarar.
Har ila yau
sanarwar ta kunshi cewa; kasar ta Rasha za kuma ta samar da kudade ga kasashen
tarayyar da suke da sha’awar sayen allurar rigakafin.
Tarayyar
Afirkan tana fatan ganin cewa adadin allurar rigakafin da ta saya daga Rasha za
ta taimaka wajen yi wa kaso 60% na mutanen nahiyar rigakafi idan aka hada da
wani adadin da ya kai miliyan 270 da ta shirya saya daga kamfanonin Johnson and
Johnson da Pfizer Astra Zeneca.
Mutanen da
su ka kamu da cutar covid-19 a nahiyar Afirka sun haura 3.79, wadanda su ka mutu kuwa sun kai
100,294, kamar yadda hukumar da ke fada da cutuka masu yaduwa a nahiyar ta
Afirka ta bayyana.