A Kalla Mutane Biyu Ne Su Ka Halaka Sanadiyyar Wani Hari Da Aka Kai A Birnin Kabul Na Kasar Afghanistan

2021-02-20 14:00:54
A Kalla Mutane Biyu Ne Su Ka Halaka Sanadiyyar Wani Hari Da Aka Kai A Birnin Kabul Na Kasar Afghanistan

Majiyar ‘yan sandan daga birnin na Kabul ta ambaci cewa; Da safiyar yau Asabar wani abu mai fashewa ya tarwatse a birnin Kabul na Afghanistan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da kuma jikkata wasu biyu.

Majiyar ‘yan sandan ta kara da cewa; Bom din farko ya tashi ne da misalin karfe 8;00 akan titin Darulaman dake yammacin birnin na Kabul, yayinda bom na biyu ya tashi bayan mintuna 15 a yankin Karte-Parwan.

Mutane biyu ne su ka rasa rayukansu, yayin da wasu biyu su ka jikkata.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai harin.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!