Biden:Amurka A Shirye Take Ta Koma Kan Yarjejeniyar JCPOA Na Kasar Iran

2021-02-20 11:21:47
Biden:Amurka A Shirye Take Ta Koma Kan Yarjejeniyar JCPOA Na Kasar Iran

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana cewa gwamnatin Amurka za ta koma cikin yarjejeniyar JCPOA ta shirin nukliyar kasar Iran, inda za ta tattauna da tokwarorinta na kasashen Turai don ganin yadda za’a raya yarjejeniyar. Shugaban ya bayyana haka ne a jiya a jawabin yayi ta yanar gizo a taron harkokin tsaro na Munich a jiya Jumma’a.

Shugaban bai yi maganar yauce ne Amurka zata daukewa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi munu wanda tsohon shugaban kasar ta ta dorawa kasar ba, bayan ficewarta daga yarjejeniyar.

A shekara ta 2015 ne gwamnatin Obama ta kulla wannan yarjejeniyar tare da wasu kasashe 5 masu kujerun din din din a MDD da kuma Jamus, yarjejeniya ta samu amincewar kwamitin tsaro na MDD tare da samar da kuduri mai lamba 2231.

Kasar Iran dai ta bayyana cewa komawar Amurka cikin yarjejeniyar ba tare da dauke mata takunkuman zaluncin da ta dorawa kasar ba bai da wani muhimmanci a wajenta.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!