Kasar Sin Ta Mai Da Martani Ga Shakkun Da Jami’An Amurka Da Birtaniya Suka Nuna Kan Rahoton WHO

2021-02-20 10:30:41
Kasar Sin Ta Mai Da Martani Ga Shakkun Da Jami’An Amurka Da Birtaniya Suka Nuna Kan Rahoton WHO

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta mayar da martani dangane da zargin da jami’an Amurka da Birtaniya suka nuna kan rahoton masanan hukumar lafiya ta duniya (WHO) dangane da bullar cutar korona a kasar, inda suka ke cewa masanan ba su gabatar da rahotonsu cikin ’yanci ba.

Gidan radiyon CRI hausa ta kasar Sin ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Sin, Hua Chunying ta na fadar haka a ranar alhamis da ta gabata, ta kuma kara da cewa, gabatar da rahoto cikin ’yancin kai ba ya nufin amincewa da abubuwan da kasashen yamma suke so na dorawa kasar Sin laifi dangane da bullar cutar ba.

A cewarta, Amurka ta bukaci Sin ta bada hadin kai ga masanan WHO, kuma a hakika dai, masanan WHO sun bayyana sau da dama kan cewa, a cikin nazarin da suka yi, kasar Sin ta ba da hadin kai sosai, kuma sun je wuraren da suke so tare da mu’ammala da mutanen da suke son tattaunawa da su kamar yadda suka ga dama.

Ha kazalika, sun ce sun samu muhimman bayanai da suke bukata, na fahimtar ta yadda cutar ta yadu. Kasashen Amurka da Burtaniya dai sun nuna shakku kan ingancin rahoton wanda ya wanke kasar Sin daga aikata wani laifi.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!