Rasha:Lokaci Yayi Na Dawowa Kan Gaskiyar Abinda Yakamata A Yi Dangane Da Yarjejeniyar JCPOA

2021-02-20 10:05:51
Rasha:Lokaci Yayi Na Dawowa Kan Gaskiyar Abinda Yakamata A Yi Dangane Da Yarjejeniyar JCPOA

Jakadan kasar Rasha a MDD ya ce, a halin yanzu ya tabbatar cewa siyasar takurawa mafi muni kan kasar Iran don tilasta mata dawowa kan sabuwar yarjejeniyar nukliya ta sha kasa, don haka ya na kira ga wadanda abin ya shafa su dawo kan hanyar diblomasiyya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Mikhail Ulyanov ya na fadar haka a birnin Vienna a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa duk wadanda suke goyon bayan takurawa kasar Iran don cimma manofofin kasar yamma a kanta sun tabbatar da cewa siyarsar takurawa kan kasar ta karye, ba kuma wata hanya da ta rage in banda ta diblomasiyya.

Kafin haka dai a jiya jumma’a ce manya-manyan jami’an tsaro na kasar Amurka daga ma’aikatar harkokin wajen kasar da kuma ma’aikatar tsaro suka tattaunawa kan yadda Amurka za ta dawo cikin yarjejeniyar JCPOA wacce gwamnatin da ta shude ta fice daga cikinta a shekara ta 2018.

Sai dai abinda tattaunawa a tsakaninsu itace, shin Amurka za ta dawo cikin yarjejeniyar kafin zaben shugaban kasa a kasar Iran wanda za’a gudanar a cikin watan Yuni mai zuwa ne ? ko kafin zaben.

Jami’an gwamnatin kasar Iran dai sun bayyana cewa basu dakatar da rage riko da takewa yarjejeniyar ba, sai idan Amurka ta dauke dukkan takunkuman tattalin arziki da ta dorawa kasar bayan ficewarta daga yarjejeniyar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!