NATO Zata Kara Yawan Sojojinta A Kasar Iraki Don Yakar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Daesh

2021-02-20 09:57:18
NATO Zata Kara Yawan Sojojinta A Kasar Iraki Don Yakar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Daesh

Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana cewa kungiyarsa za ta kara yawan sojojinta a kasar Iraki don abinda ya kira yaki da kungiyar Daesh.Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jens Stoltenberg ya na fadar haka a jiya Alhamsi, ya kuma kara da cewa kungiyar za ta yi haka ne tare da bukatar gwamnatin kasar ta Iraki.

Stoltenberg har’ila yau ya kara da cewa ga dukkan alamu mayakan kungiyar ta Daesh su na son sake dawowa kasar ta Iraki, ganin yadda hare-hare ta’addanci suke kara yawa a cikin ‘yan watannin da suka gabata.

Kafin haka dai majalisar dokokin kasar ta Iraki ta bukaci ficewar sojojin kasashen waje daga kasar musamman sojojin Amurka, saboda kissan da shugaban kasar Amurka da ya shude yayi wa shuwagabannin gwagwarmaya da kungiyar ta Daesh a kasar Iraki Janar Shahid Kasim Sulaimani da kuma Mahdi Almuhandis a farkon shekara da ta gabata.

A halin yanzu dai Amurka tana da sojojin 2,500 a wurare daban-dan a kasar ta Iraki. Babban sakataren ta kungiyar tsaro ta NATO ya ce ya na saran yawan sojojin NATO a kasar Iraki zai tashi daga 500 zuwa 4000 nan gaba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!