Skocic:Muna Iya Kokarimmu Na Horasda Kungiyar Kwallon Kafa Ta Kasar Iran

2021-02-20 08:48:40
Skocic:Muna Iya Kokarimmu Na Horasda Kungiyar Kwallon Kafa Ta Kasar Iran

Babban kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar Iran Dragan Skocic ya bayyana cewa suna kokarin ganin sun horasda ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa na kasar don ganin sun sami nasara a wasannin daukar kofin duniya na shekara ta 2022. Jaridar ‘Iran news’ ta nakalto Skocic babban mai horasda ‘yan wasan ya na fadar haka a Tehran.

Skoci, ya kuma kara da cewa a halin yanzu sun dakatar da horaswa zuwa watan Yuni na wannan shekara a lokacinda hukumar wasannin kwallon kafa ta Asia (AFC) za ta bayyana tsarin fidda gwanin wasannin na shekara ta 2022.

Skocicc ya kara da cewa a halin yanzu dai, shi da sauran masu horasda yan wasan kasar Iran suna kallon wasanni daban-dabn don zaben wadanda suka dace da su. Sannan idan an fitar da jadawalin wassanin gasar ta shekara ta 2022 za su fara horaswa daga ciki har da wasanni da wasu kungiyoyin kwallon kafa na abota.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!