Imam Khamnei: Iran Tana Da Karfin Da Za Ta Iya Dakile Dukkanin Makirce-Makircen Makiya

2021-02-18 22:06:51
Imam Khamnei: Iran Tana Da Karfin Da Za Ta Iya Dakile Dukkanin Makirce-Makircen Makiya

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullahil-Uzmah Sayyid Ali Khamnei ya wanda ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa; Makiya suna mayar da hankali ne akan wuraren da muke da rauni, sannan kuma suna shelanta yakin kwakwalwa a kanmu.

Jagoran juyin musulunci ya kuma yi ishara da cewa Iran ta fuskanci adawa da kiyayya daga manyan kasashen masu takama dakarfi da suka hada da Tarayyar Soviet, tun tun farkon cin nasarar juyin musulunci, haka nan kuma daga kasashen da suke biyayya a gare su.

Ayatullah Imam Ali Khamnei ya kuma ce; A wancan lokacin duniya ta kasu gida biyu a tsakanin kasashen da suke takama da karfi da kuma wadanda ake dannewa, amma jahuriyar musulunci ta Iran ta karya waccan ka’idar, da hakan ya sa suka bude gaba da ita.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana cewa; Da akwai ci gaba mai yawa da Iran din ta samu wadanda har yanzu kafafen watsa labaru ba su dauki labaransu ba.

Dangane da zaben da ke tafe na shugaban kasa, Jagoran juyin musulunci na Iran din ya ce wata babbar dam ace a gaban al’umma da bai kamata a yi watsi da ita ba,domin za ta bunkasa ci gaban kasa da kuma dakile duk wani fata na makiya.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!