Shugaban Kasar Iran Hassan Rauhani Ya Kira Yi Amurka Da Ta Koma Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya

2021-02-18 22:03:26
Shugaban Kasar Iran Hassan Rauhani Ya Kira Yi Amurka Da Ta Koma Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya

Shugaban na Kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya kira gwamnatin Amurka da ta yi aiki da nauyin da ya rataywa a wuyanta dangane da yarjejeniyar Nukiliya, kuma ta yi aiki da kudurin MDD, mai lamba 2231.

Shugaban na kasar Iran ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar da wasu sabbin kamfanoni a yau Alhamis.

Har ila yau shugaban na kasar Iran ya yi ishara da irin matsin labarin da Amurkan take yi wa jamhyuriyar musulunci ta Iran, yana mai nuna fatansa na ganin sabuwar gwmanatin Amurka ta biya Iran fansar asadar da ta haddasa ma ta.

Wani sashe na jawabin shugaban kasar ta Iran ya kuma bayyana cewa; Aiki da doka da yarjeniyoyin kasa da kasa, daya ne daga cikin nauye-nauyen da su ka rataya akan kowace kasa, don haka muna fatan ganin sun yi aiki da dokokin domin samun kyakkyawan yanayi a duniya.”


031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!