Guardian: Shugaban Kasar Amurka Joe Biden Yana Kokarin Kawar Da Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya

Jaridar Guardian ta kasar Birtania, bugun yau Alhamsi ta rubuta wani rahoto da yake cewa; Gwamnatin Amurka tana son ganin Saudiyya ta sauya salon takunta a alakarta, sabanin yadda ta kasance a lokacin mulkin Trump.
Har ila yau jaridar ta ce;’ Shugaban kasar Amruka Biben zai rika yin alaka ne kai tsaye da sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulazizi, bad a yarima mai jiran gado ba, Muhammad Bin Salman.
Bugu da kari, jaridar ta Birtaniya ta nakalto
sakatariyar watsa labaru ta fadar mulkin Amurka “White House” Jennifer Rene Psaki tana
cewa; Sarkin Saudiyya shi ne takwaran Biden ba dansa Muhammadu Bin Salman ba,
kuma gwamnatin yanzu tana son yin matsin lamba ga Saudiyya domin ta sauya
tsarin halifanci a kasr da kuma rage
mukamin da Muhammad Bin Salman yake da shi.
A gefe daya wani tsohon jami’in kungiyar leken asirin
Amurka, ( CIA), Bruss Lead Inn ya bayyana cewa; Sakon da Biden yake aikewa masu
mulkin Saudiyya shi ne; Matukar Muhammad Bin Salaman ne yarima mai jiran gado,
to za mu ci gaba da hulda da Saudiyya a matsayin bijirarriyar kasa.”
Har ila yau ya kara da cewa; Ban san abinda gwamnatin
Biden take tunani ba, amma ina jin zai yi wa Saudiyya kyau, idan ta sauke Bin
Salman, kuma zai iya komawa kasar Faransa da zama idan ya yi murabus.