Najeriya: Mutane 869 Sun Kamu Da Korona A Jiya Laraba

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum
869 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba, sannan kuma mutum 8
suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.
Yanzu mutum 149,369 suka kamu da
cutar a Najeriya, mutum 125,722 sun warke, 1,787 sun rasu. Sannan zuwa yanzu
mutum 21,860 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Talata, mutum 1,368 suka kamu
a Najeriya, jihohin Anambra, Oyo, Benue, Rivers da Babban birnin Tarayya, Abuja
ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin
kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa za a yi wa
mutum miliyan 109 allurar rigakafin cutar korona daga nan zuwa shekaru biyu
masu zuwa.
Ya ce gwamnati na sa ran karbar
kwalaben maganin rigakafin miliyan 57 daga AVATT da COVAX da kuma wasu miliyan
1.5, da 100,000 wanda kamfanin MTN da kuma kasar India suka baiwa Najeriya a matsayin gudunmawa, wanda za a yi amfani da
su wajen yi wa wadanda suka dara shekaru 18 allurar rigakafi a Najeriya.
Wadanda za su kasancea sahun farko wajen samun allurar rigakfin dai
su ne, Mata masu ciki, ma’aikatan kiwon lafiya, jami’an tsaro, tsofaffi da kuma marasa lafiya
015