​Porto Ta Lallasa Juventus Da Ci 2 – 1 A Wasannin Cin Kofin zakarun Nahiyar Turai

2021-02-18 13:02:19
​Porto Ta Lallasa Juventus Da Ci 2 – 1 A Wasannin Cin Kofin zakarun Nahiyar Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Porto ta kasar Portugal ta lallasa Juventus ta kasar Italiya da ci 2 – 0, a ci gaba da wasannin ccin kofin nahiyar turai.

Wasan wanda aka buga a jiya Laraba ya bayar da mamaki kan yadda dan wasan kasar Iran Mehdi Tarmi da ke wasa a kungiyar kwallon kafa ya zura wa Juventus kwallo ta farko a raga a cikin kasa da minti daya da fara wasan, a filin wasanni na Dragao a kasar Portugal.

Wasan dai ya dauki hankali matuka, musamman ganin cewa Critiano Ronaldo yana buga wasa a Juventus, kuma yana kara wa ne da Porto kungiyar wasan kwallon kafa da ke kasarsa Portugal, inda aka tashi wasan 2 – 1, ba tare da Juventus ta iya farkewa ba.

Haka lamarin ya kasance ga kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kasar Spain a wasan da ta buga da PSG ta kasar Faransa, inda Paris St Germain din ta casa kungiyar Barcelona da ci 4-1 a cikin gidan Barcelona.

Kaftin din Barcelona Lionel Messi ne ya fara zura kwallo a ragar PSG wadda ta buga wasan karshe a bara a irin wannan gasa tare da Bayern Munich, inda Bayern Munich ta doke ta 1-0 . sannan bayan da Messi ya fara cin kwallo a minti na 27 da fara wasan, PSG ta kara matsa kaimi inda ta farke ta hannun Kylian Mbappe, sannan kuma ya kara ta biyu.

Dan kwallon Eberton, Moise Kean da ke buga wasan aro a PSG ne ya kara saka kwallo ta uku, duk da cewa Bercelona ta yi ta kai kora, amma hakan bai haifar da da mai ido, inda daga karshe Mbappe ya sake zura wa PST kwallo ta hudu, kuma kwallonsa ta uku da ya zura a wasan, kuma har aka tashi Barcelona ba ta iya farkwewa ba.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!