Shugaba Ruhani Ya Caccaki Kasashen Turai Kan Yarjejeniyar Nukiliya

2021-02-18 09:51:23
Shugaba Ruhani Ya Caccaki Kasashen Turai Kan Yarjejeniyar Nukiliya

Shugaba Hassan Rohani na Iran, ya caccaki kasashen turai kan rashin cika alkawuran da suka dauka game da yarjejeniyar nukiliyar 2015.

Yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da yammacin jiya Laraba, shugaba Ruhani, ya ce shigar da wasu sabbin sabbin batutuwa a cikin yarjejeniyar ta 2015, abu ne wand aba zai taba yiyuwa ba.

Dakta Ruhani, ya ce yarjejeniyar da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya, da kwamitin tsaron MDD, ya amince da ita, kana kuma aiki ne na tsawon shekaru na tsakanin Iran da sauren kasashen duniya shida wanda aka cimma bisa jituwa.

A hannu daya kuma shugabanin Ruhanin, ya bayyana cewa hanya daya ce ta ragewa kasashen turai idan suna son ceto yarjejeniyar shi ne su nuna da gaske su ke, kuma a aikace, sannan ya kara da cewa wata hanyar ta kare yarjejeniyar ita ce dagewa Iran takunkuman rashin Imani da Amurka ta kakana mata.

A nata bangare shugabar gwamatin ta Jamus Angela Merkel, ta nuna matukar damuwa game da makomar yarjejeniyar inda ta ce yana da mahimmanci a ci gaba da kare yarjejeniyar a matsayinta ta kasa da kasa, tare da bukatar a warware sabanin dake akwai ta hanyar tattaunawa.

Ta kuma yi fatan kara karfafa alaka tsakanin Iran da Jamus, da kuma sauren kasashen yankin dana asiya don samar da zaman lafiya da tsaro.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!