Amurka Da Turai Zasu Tattauna Kan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

2021-02-18 09:44:45
Amurka Da Turai Zasu Tattauna Kan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

A wani lokaci yau Alhamis ne ministan harkokin waken kasar Faransa, Jean-Yves Le Drian, zai karbi bakuncin takwarorinsa na Jamus da Biritaniya a wani yunkuri na tattaunawa domin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Shi ma sakataren harkokin wajen Amurka, zai halarci taron amma ta kafar bidiyo.

Tun dai bayan da tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya fice daga yarjejeniyar ne a shekarar 2018, aka shiga takun tsaka game da makomarta inda Iran a nata bangare ta daina aiki da wasu bangarori da yarjejeniyar ta 2015 ta kunsa a matsayin maida martani ga ficewar Amurka dama jerin takunkuman da Amurkar ta lafta mata.

A halin da ake ciki dai sabuwar gwamnatin Amurka ta ce ba zata janye wa Iran takunkumi ba har sai Iran din ta dakatar da matakan da take dauka kan yarjejeniyar, yayin da ita ma Iran din ta ce duk wannan ba zai faru ba har sai Amurka ta dage mata gabadayen takunkuman da tsohuwar gwamnatin Amurka ta kakaba mata.

Ko a jiya Laraba, jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayyatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bukaci gani-a-kasa, ba wai magana da fatar baki ba ko kuma alkawura game da yarjejeniyar nukiliyar.

A kwanan baya dai Jamus ta bakin ministan harkokin wajenta ta bukaci a sanya shirin Iran na makamman masu linzami a cikin ababen da za a tattauna akansu, game da yarjejeniyar.

Ita kuwa a nata bangare faransa, ta bukaci da a sanya kasashen yankin musamman Saudiyya har ma da Isra’ila a cikin tattaunawar da suke fatan yi nan gaba kan yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran.

Saidai Iran ta dage akan cewa babu batun sake tattaunawa akan yarjejeniyar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!