Sudan Ta Kirayi Jekadanta A Habasha Domin Tuntuba

2021-02-18 09:30:59
Sudan Ta Kirayi Jekadanta A Habasha Domin Tuntuba

Kasar Sudan ta sanar da kiran jekadanta a Habasha, a daidai lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu ke kara tsami a iyakarsu.

Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan, Mansour Boulad, ya ce kasar ta kirayi jekadan na ta ne domin tuntubarsa game da alakar dake tsakanin kasar da Habasha.

Kuma a cewarsa jekadan ba zai koma ba har sai an gama tuntubarsa game da batutuwan da suka shafi alakar kasashen biyu.

Matakin na gwamnatin Khartoum, na zuwa ne a daidai lokacin da takkadama tsakanin kasashen biyu ke kara tsami game da yankin nan na El-Fashaga wanda ko wane daga cikin manoman kasashen biyu ke cewa mallakinsa ne.

Kafin hakan dai a ranar Lahadi data gabata Sudan, ta zargi Habasha da baiwa sojojinta izinin shiga kasar, wanda gwamnatin Khartoum ta danganta da tsokana.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!