Najeriya:Buhari Ya Bukaci Jami’an Tsaro Su Kubutar Da ‘Yan Makarantan Da Aka Tsare A Naija

2021-02-17 22:18:25
Najeriya:Buhari Ya Bukaci Jami’an Tsaro Su Kubutar Da ‘Yan Makarantan Da Aka Tsare A Naija

Shugaban kasar tarayyar Najeriya Mohammadu Buhari ya bukaci jami’an tsaron kasar wadanda suka hada da sojojin da kuma ‘yan sanda da su gaggauta kubutar da ‘yan makaranta da kuma malamansu wadanda ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane suka tsare a jihar Naija a jiya Talata.

Shugaban ya bayyana haka ne a safiyar yau Laraba ta bakin Shehu Garba jami’I mai bashi shawara kan al-amuran watsa labarai a fadar shugaban kasa.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa yan bindigan san kama yan makarantar da malaman sakandarin Kagara na karamar hukumar Rafi a jihar Naija ne a jiya da yamma, kuma har yanzu ba’a san adadin daliban da kuma malaman da aka kamanba.

Amma wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyana cewa wadanda suka tafi da su cikin daji suna sanye da kayan sarki ko kayan soja.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!