Tunisia:Kungiyar Yan Kasuwa Sun Bukaci Hadinkai Don Warware Rikicin Kundin Tsarin Mulkin Kasar

2021-02-17 22:11:57
Tunisia:Kungiyar Yan Kasuwa Sun Bukaci Hadinkai Don Warware Rikicin Kundin Tsarin Mulkin Kasar

Kungiyar yan kasuwa mafi girma a kasar Tunisia ta bukaci yan siyasa da kuma gwamnatin kasar su hada kai don gaggauta kawo karshen matsalar rashin majalisar ministoci a kasar kafin al-amura su kara tabarbarewa.

Kamfanin dillancin labaran Anotoly na kasar Turkiya ya kara da cewa kungiyar ta yi wannan kiran ne a yau Laraba, inda ta bukaci hadin kai tsakanin ‘yan siyasar kasar don fidda kasar a cikin tsaka mai wuya da ta fada ciki.

Har’ila yau kungiyar ta bukaci kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka don ganin an fita cikin rikicin kundin tsarin mulki wanda ya hana samar da majalisar ministoci a kasar.

Makonni biyu kacal da rantsar da ministoci 11 a gwamnatin firai minister Al-Mushishi sai ya sauke wasu daga cikinsu ya kuma maye gurbinsu da wasu, wanda hakan ya kara rikita harkokin siyasar kasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!