Imam Khamenei: Juyin Juya Halin Muslunci Ya Wanzu Ne Sakamakon Imani, Juriya, Da Sadaukarwa

2021-02-17 12:46:29
Imam Khamenei: Juyin Juya Halin Muslunci Ya Wanzu Ne Sakamakon Imani, Juriya, Da Sadaukarwa

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Imam Khamenei ya bayyana cewa, juyin juya halin muslunci a Iran ya wanzu ne sakamakon juriya, sadaukarwa da kuma imani da Allah madaukakin sarki.

Jagoran ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a yau, dangane da zagayowar lokacin tunawa da irin sadaukarwar da al'ummar birnin Tabriz da ke yankin Azerbaijan suka yi a lokacin yunkurin juyin juya halin muslunci a kasar.

Ya ci gaba da cewa, juyin juya halin Iran ya zama wani karfen kafa da ya hana kasashe masu girman kai cimma manufofinsu a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya.

Dangane da batun yarjejeniyar nukiliya kuwa ya bayyana cewa, daga yanzu Iran ba za ta sake amincewa da maganganu ko alkawulla ba, dole ne maganganu da alkawulla su zama tare da aiki a lokaci guda.015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!