Amurka Ba Za Ta Tattauna Da Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman Ba

Gwamnatin Amurka ta ce za ta tattaunawa
da Saudiyya, amma da sarkin kasar Salman Bin Abdulaziz kawai, ba da yarima
Muhammad Bin Salman ba.
Tashar RT ta bayar da rahoton cewa,
a lokacin da take zantawa da manema labarai a yammacin jiya, mai magana da
yawun fadar White House a kasar Amurka Jane Psaki, ta bayyana cewa a
halin yanzu babu wani shiri na tattaunawa da Saudiyya.
Ta ce idan har shugaba Joe Biden zai
yi wata tattaunawa da Saudiyya, to zai tuntubi sarkin kasar ne Salman Bin
Abdulaziz, ba dansa yarima Muhammad Bin Salman ba.
Ta ci gaba da cewa, ko shakka babu
akwai canje-canje a cikin siyasar sabuwar gwamnatin Amurka dangane da kasar
Saudiyya, amma duk da haka bangarorin biyu za su ci gaba da yin aiki tare a
wasu bangarori, musamman ma taimaka Saudiyya ta fuskar kariya.
A kwanakin baya an tambayi Jane
Psaki kan ko Joe Biden na niyyar kakaba wa gwamnatin Saudiyya takunkumi kan kisan
Jamal Khashoggi, amma ta ki amsa wannan tambaya.
Gwamnatocin kasashen Saudiyya da
Hadaddiyar Daular Larabawa UAE dai sun mara baya ido rufe ga tsohon shugaban
kasar Amurka Donald Trump a lokacin yakin neman zabe, da nufin ganin ya samu
nasarar kayar da Joe Biden a zaben, wanda hakan hakan ya sanya gwiwar
mahukuntan wadannan kasashe ta yi sanyi dangane da makomar alakarsu da Amurka, bayan
da Trump ya sha kayi a zaben.
015