Kasar India Za Ta Shiga Cikin Atisayen Soja Da Iran Za Ta Yi Da Kasahen Rasha Da China

2021-02-16 20:54:08
Kasar India Za Ta Shiga Cikin Atisayen Soja Da Iran Za Ta Yi Da Kasahen Rasha Da China

Kwamandan sojan ruwa na Iran, Admiral Hussain Khanzadi ne ya sanar da cewa; Manufar atisayen da za a yi a doron ruwan tekun India, shi ne samar da tabbatar da tsaro na bai daya, kuma India ma ta amince za ta shiga a yi da ita.

A yau Talata ne dai aka fara atisayen sojan ruwan a tsakanin kasashen na Iran, Rasha, da China.

Kwamandan sojan ruwan na Iran ya bayyana India a matsayin daya daga cikin kasashe masu karfin soja a yankin, da hakan ne ya sa za shiga atisayen da za a yi.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Iran ta yi atisayen soja karo na biyu na hadin gwiwa da kasashen Rasha da China. An yi atisayen farko a watan Disamba na 2019.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!