Duk Wanda Shekarunsa Su Ka Kai 65 Za A Rika Kula Da Lafiyarsa Kyauta A Iran

2021-02-16 20:49:06
Duk Wanda Shekarunsa Su Ka Kai 65 Za A Rika Kula Da Lafiyarsa Kyauta A Iran

Hukumar da take tallafawa rayuwar al’umma ( Social Security) ta Iran, ta sanar da cewa; Daga yanzu dukkanin ‘yan kasar da shekarunsu su ka kai 65 za a yi musu magani ne kyauta.

A yayin wani taro da ma’aikatar ta yi a yau Talata,mataimakin shugabanta Amir Abbas manochehry ne ya sanar da hakan.

Har ila yau ya ce; Matakin da aka dauka zai haifar da gagarumin sauyi a fagen harkar lafiya.

Mafi yawancin al’ummar Iran dai suna da inshore ta kiwon lafiya wacce take samar musu da sauki mai yawa wajen samun magani a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!