Kasar Guinea Ta Fara Jan Damarar Fada Da Sake Bullar Cutar Ebola

2021-02-16 20:38:09
Kasar Guinea Ta Fara Jan Damarar Fada Da  Sake Bullar Cutar Ebola

Wakilin kungiyar lafiya ta duniya ( WHO) a kasar ta Guinea, Dr. George Alfred Ki- Zerbogives ne ya sanar da shiry-shiryen da ake yi a kasar domin fuskantar cutar ebola da ta sake bulla wacce kuma ya zuwa yanzu ta ci rayukan mutane biyar.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Guinea din ta tabbatar da mutuwar mutane 5 daga cutar da ta bulla a cikin ‘yan kwanakin nan.

Dr. George Alfred ya kuma ce; Da akwai kyakkyawan fatan za a samu nasarar dakile cutar cikin gaggawa saboda an dauki darussa da dama a lokutan da su ka gabata.

Kasar Guine suna daga cikin kasashen da su ka yi fama da cutar Ebola a shekarun baya.
031


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!