Araqchi: Iran Za Ta Tattauna Da Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya Ne Kawai Kan Sha’anin Yankin

Mataimakin ministan harkokin wajen
kasar Iran ya bayyana cewa, kasar za ta tattauna kan batutuwan da suka shafi
yankin gabas ta tsakiya ne kawai tare da kasashen yankin.
Mataimakin ministan harkokin wajen
kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa, Iran a shirye take ta tattauna
da dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya dangae da batutuwa da suka shafi
yankin, da kuma yadda za a warware matsalolin da suka addabi al’ummomin yankin.
Araqchi ya ce; Iran ba za ta amince
wasu banagrori da ba na yankin ba su shiga cikin irin wannan tattaunawa, domin
kuwa matsaloli da dama da ake fama da su a yankin gabas tsakiya an kirkiro su
ne daga wajen yankin.
Ya kara da cewa, yanzu haka akwai
tattaunawa da take gudana tsakanin wasu kasashen yankin da kuma Iran, kan yadda
za a fuskanci lamurra musamman a bangaren tsaron yankin, kan yadda za a gudanar
da ayyuka na hadin gwiwa a tsakaninsu.
Iran ta sha nanata cewa kasashen
yammacin turai da wasu kasashen larabawan yankin suka dogara da su domin su
tabbatar musu da tsaro, hakan ba ita ce mafita ba, babbar mafita ita ce samun
hadin kai da fahimtar juna tsakanin dukkanin kasashen yankin, da kuma yin aiki
tare a dukkanin bangarori da hakan ya hada har da bangaren tsaro.
015