​Okonjo-Iweala: WTO Za Ta Mayar Da Hankali Kan Matsalolin Da Corona Ta Haifar Wa Tattalin Arzikin Duniya

2021-02-16 13:21:39
​Okonjo-Iweala: WTO Za Ta Mayar Da Hankali Kan Matsalolin Da Corona Ta Haifar Wa Tattalin Arzikin Duniya

Sabuwar babbar darakta ta kungiyar kasuwanci duniya Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana cewa, za su mayar da hankali kan tarnakin da cutar corona ta jawo wa harkokin tattalin arzikin duniya.

Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana hakan ne bayan zabenta da aka yi jiya a matsayin babbar darakta ta kungiyar kasuwanci ta duniya WTO, inda ta zama ‘yar Afirka ta farko kuma mace ta farko da ta hau kan wannan kujera a tarihi.

Ngozi wadda tsohuwar ministar kudi ce a Najeriya, kuma tsohuwar manajan darakta ta bakin duniya, ta samu goyon bayan kasashe da dama tun lokacin da ta fito takarar neman wannan kujera a shekarar da ta gabata, amma tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya tsaya kai da fata yaki amincewa da hakan.

Sai dai sabon shugaban kasar Amurka Joe Biden ya amince da takarar Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin babbar darakta ta kungiyar WTO, inda a jiya kuma kwamitin mutane 9 mai zaben shugaba a wanann kungiya, ya tabbatar da ita a matsayin wadda aka zaba a kan kujerar shugabancin kungiyar.

Ngozi ce dai ta taka muhimmiyar rawa a lokacin da take ministar kudi ta Najeriya a lokacin shugabancin Obasanjo, wajen ganin an yafe wa Najeriya makudan kudin da ake bin ta bashi, kuma daga karshe ta samu nasara a kan hakan.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!