Iran Da Qatar Sun Jaddada Wajabcin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin

2021-02-16 09:54:30
Iran Da Qatar Sun Jaddada Wajabcin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin

Ministan harkokin wajen kasar Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, ya fara wata ziyarar aiki a nan birnin Tehran.

Yayin ziyarar tasa ya gana da takwaransa Muhammad Jawwad Zarif, da kuma shugaban kasar ta Iran Hassan Ruhani.

Yayin ganawar shugaba Ruhani, ya bayyana cewa har kullun Iran, na fatan samar da zaman lafiya a mashigar Ormuz, kuma zaman lafiya da tsaro ba zai taba samuwa ba, ba tare da hadin guiwa ba tsakanin kasashen yankin, kuma kasashen yankin ne ya kamata su samar wa kansu da kansu mafita ta hanyar daukan matakan da zasu amfane su nan gaba.

Shi ma dai a nasa bangare ministan harkokin wajen kasar ta Qatar, ya ce kasarsa na yarda irin kokarin da Iran ke yi a yankin, wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Ya kuma bukaci Kasashen yankin da su magance sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa, haka zalika ya yi fatan Amurka za ta dawo cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran, tare da dage wa Iran takunkumi wanda hakan zai taimaka wajen kawo karshen duk wata takkadama.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!