Chadi Za Ta Aike DaKaru 1,200 A Iyakar Nijar, Mali Da Burkina

2021-02-16 09:39:27
Chadi Za Ta Aike DaKaru 1,200 A Iyakar Nijar, Mali Da Burkina

Shugaba Idriss Deby Itmo, na Chadi, ya sanar da cewa kasarsa za ta aike da dakaru 1,200 a iyakar nan da ake kira ta kasashe guda uku, wato Nijar, Mali da kuma Burkina Faso, domin yakar gungun kungiyoyin dake kiran kansu na jihadi.

Wannan matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta Chadi ke karbar taron shuwagabannin kasashen kungiyar G5 Sahel, da aka fara jiya a birnin N’Djamena.

Taron dai na maida hankali ne kan yadda za’a hada karfi da karfe domin kawo karshen ‘yan ta’adda da suka addabi yankin, da kuma batun samar da ci gaba.

A wani lokaci yau Talata za’a ci gaba da taron ta hanyar fadada shi inda zai samu halartar wasu kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa dake taimakawa kasashe mambobin kungiyar ta G5 Sahel.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!