Amurka Na Shirin Cire Kungiyar Ansarullah Daga Jerin ‘Yan Ta’adda

2021-02-16 09:23:40
Amurka Na Shirin Cire Kungiyar Ansarullah Daga Jerin ‘Yan Ta’adda

A wani lokaci yau Talata ne gwamnatin Amurka za ta sanar da cire kungiyar Ansarullah ta Yemen da akafi sani da ‘yan Houtsis daga cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda, wata guda bayan da tsohuwar gwamnatin Trump ta ayyana kungiyar a mtasayin ta ‘yan ta’adda’.

Matakin dai tamakar watsi ne da matakin da tsohuwar gwamnatin Trump, ta dauka kan ‘yan Houtsin.

Sanya kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda da tsohuwar gwamatin ta yi, ya fuskanci kakkausan martani a ciki daga wajen Amurka.

Saidai Saudiyya ta ce har yanzu tana kallon ‘yan Houtsis a matsayin ‘yan ta’adda, tare kuma da nuna fishinta kan yadda kawarta Amurka ta juya mata baya kan yakin da ta ke jagoranta a Yemen.

A baya baya nan rikici ya kaure tsakanin bangarorin dake yakar juna a Yemen musamman a yankin Marib wanda ya kunshi arzikin man fetur, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane, sai kuma hare haren da ‘yan Houtsi ke kai wa Saudiyya.

Amurka dai na mai tir da hare haren da ‘Yan Houtsi ke kai wa Saudiyya musamman a baya baya nan, kuma ta ce matakin soke kungiyar daga jerin ‘yan ta’adda bai shafi jagororin kungiyar ta ‘yan Houstis ba.

Kasashen duniya da dama da Kungiyoyin kasa da kasa musamman na agaji sun nuna damuwa matuka da matakin tsohuwar gwamnatin Amurka na sanya ‘yan Houtsi a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda wanda suka bayyana cewa zai maida hannun agogo baya a yunkurin samar da zaman lafiya a kasar ta Yemen da yakin kusan shekaru shida ya daidaita.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!