Yemen:Jiragen Yaki Wadanda Ake Sarrafasu Daga Nesa Sun Kai Hare-Hare A Kan Biranen Jidda Da Abha Na Kasar Saudiya

2021-02-15 22:05:44
Yemen:Jiragen Yaki Wadanda Ake Sarrafasu Daga Nesa Sun Kai Hare-Hare A Kan Biranen Jidda Da Abha Na Kasar Saudiya

Kakakin sojojin kasar Yemen Yahyah Saree ya bada sanarwan cewa jiragen yakin kasar wadanda ake sarrafasu daga nesa sun kai hare-hare kan tashoshin jiragen sama na Jidda da kuma Abhah a cikin kasar Saudiya tare da samun nasara a hare-hare.

Tashar talabijin ta AL-Mayadeen da ke kasar Lebanon ya nakalto Saree ya na fadar haka a safiyar yau Litinin ya kuma kara da cewa, sojojin kasar sun maida martani ne ga hare-haren kasashen saudiya da kawayenta kan mutanen kasar Yemen na baya-bayan nan, da kuma saboda ci gaba da killace kasar wanda wadannan kasashe suke yi.

Yahyah Saree ya kara da cewa wannan shi ne hare-hare na 5 a cikin kwanaki biyar a jare da suke kai hare-hare kan wurare daban-daban a cikin kasar ta saudiya.

Har’ila yau bayan wannan labarin kafafen yada labarai na kasar saudiya sun bada sanarwan cewa sojojin kasar ta Saudiya sun kakkabo jiragen yakin na kasar ta Yemen a tsakanin garuruwan Khamis da Mashid kafin su kai ga bararsu ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!