Barham Saleh:Zaman Lafiya A Yankin Kudancin Asia Ba Zai Yu Ba Sai Tare Da Zaman Lafiya A Kasashen Iraki Sa Siriya

Shugaban kasar Iraki Barhama Saleh ya bayyana cewa samun zaman lafiya a yankin Asiya ta kudu zai samu ne kawai idan zaman lafiya ta dawo a kasashen Iraki da Siriya.
Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Saleh ya na fadar haka a lokacin da yake ganawa da Jakadan kasar Siriya a Iraki, Sutam Jad’an a fadarsa ta (Assalam) a safiyar yau Litinin a birnin Bagdaza.
Shugaban kasar ta Iraki ya jaddada muhimmancin aiki tare a tsakanin kasashen biyu don ganin zaman lafiya ya dawo a yankin, sannan sun bukaci fadada harkokin kasuwanci tsaro da sauransu a tsakanin kasashen biyu makobtan juna.
A halin yanzu dai kasashen biyu su na cikin yarjejeniyar kasashe 4 na yankin wadanda suke musayar bayan tsaro a tsakaninsu don murkushe kungiyoyin ‘yan ta’adda. Kasashen sun hada da Rasha, Iran, Siriya da kuma Iraki.
An kulla wannan yarjejeniyar ce tsakanin kasashen 4 shekaru 5 da suka gabata.
A shekara ta 2014 mayankan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh suka mamaye wasu yankuna masu yawa a kasashen Iraki da Siriya, amma gwamnatocin wadannan kasashe 4 da kungiyar Hizbullah ta Lebanon samu nasarar kwato kasashen biyu daga hannun wadanan kungiyoyi.