Najeriya : An Saka Dokar Hana Fita A Oyo Saboda Rikicin Kabilanci

2021-02-15 15:07:45
Najeriya : An Saka Dokar Hana Fita A Oyo Saboda Rikicin Kabilanci

Gwamnati jihar Oyo ta rufe kasuwar kayan gwari da ke Sasa a garin Ibadan, kana ta kafa dokar hana fita a yankin da ke karamar hukumar Akinyele.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin gwamnatin jihar Oyo, Taiwo Adisa, da aka raba wa manema labarai, ya ce gwamanatin jihar Oyo ta kafa dokar hana fita daga shida na yamma zuwa karfe bakwai na safe a yankin.

Shi ma dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta kare dukkan mabiya addinai da dukkan kabilun kasar - ko da kuwa suna da rinjaye a yankin da suke rayuwa - ko kuma tsiraru ne su, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadar, kamar yadda wata sanarwa da Mallam Garba Shehu, mai ba shugaban Najeriyar shawara kan kafofin yada labarai ya fitar a jiya Lahadi.

Rikicin dai a cewar rahotanni ya yi sanadin mutuwar mutane da kuma hasarar dukiyoyi.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!