Iran : Za'ayi Wa Jama’a Kashi 70% Riga Kafin Korona A Kakar Bana

2021-02-15 15:03:48
Iran : Za'ayi Wa Jama’a Kashi 70% Riga Kafin Korona A Kakar Bana

Hukumomin kiwon lafiya a Iran, sun bayyana cewa suna fatan yi wa jama’ar kasar kasha 70% allurar riga kafin cutar korona kafin kasrhen kakar bana.

Da yake sanar da hakan shugaban kwamitin masani kimiya ya yaki da cutar ta korona, Mostafa Ghanei, ya ce ana bukatar alluran riga kafin cutar kimanin miliyan 160 domin yi wa jama’ar kasar riga kafi.

Ko wacce kwalba allurar riga kafin cutar na kamfanin Sputnik-V, ya tasawa gwamnatin kasar dalar Amurka 4 zuwa 5.

Game da riga kafin korona na kamfanin Pfizer, Iran ta ce kamfanin yak i mika mata magungun cutar canser data saya, wanda kuma a cewarsa na daga cikin abunda ya sanya Iran ta ki sanya rigakafin na Pfizer, baya ga hakan kuma maganin yana da wuyar sha’ani wajen jigila da adanonsa saboda yana bukatar zama cikin sanyi mai daraja kasa da -70 Wanda kuma shi ma wani babban kalubale ne.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!