Taron Shugabannin G5 Sahel Kan Ayyukan Ta’addanci

2021-02-15 15:01:34
Taron Shugabannin G5 Sahel Kan Ayyukan Ta’addanci

Shugabannin Kasashen Kungiyar G5 Sahel na taronsu karo na bakwai a birnin N’Djamenan Chadi kan batun ayyuakan ta’addanci.

Taron da ya hada shugabannin kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Jamhuriyar Nijar, zai samu halartar shugaba Emmanuel Macron na Faransa ta kafar bidiyo.

Wannan shi ne karo na farko da ake gudanar da taron bayan da Faransa ta kara yawan dakarunta a bara.

Shugaba Macron na Faransa a watan jiya ya bayyana shirin sake fasalin ayyukan sojin kasar.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!