Sudan Ta Yi Allawadai Da Kutsen Da Sojojin Habasha Suka Yi A Cikin Kasarta

Gwamnatin kasar Sudan ta yi tir da
Allawadai da kakkausar murya kana bin da ta kira kutsen da sojojin kasar
Habasha suka yi a cikin kasarta.
A cikin wani bayani da ma’aikatar
harkokin wajen kasar Sudan ta fitar ta bayyana cewa, kutsen da sojojin kasar
Habasha suka yi ta hanyar tsallaka iyakokin kasashen biyu zuwa cikin kasar ta
Sudan ya saba wa dukkanin dokoki da ka’idoji na kasa da kasa.
Bayanin ya kara da cewa, yanzu haka
akwai sojojin Habasha jibge a kan iyakokin Sudan bayan da wasu daga cikinsu
suka yi kutse a cikin Sudan, tare da aiwatar da wasu ayyuka na wuce gona da
iri.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta
Sudan ta ce tana yin kira ga mahukuntan kasar Habasha da su rungumi hanyar
zaman lafiya da girmama juna tsakaninta da Sudan, kasantuwar kasashen biyu
makwabtan juna ne.
Tun bayan rikicin da ya barke a ‘yan watannin baya a yankin Tigray na kasar Habasha, dubban mutane suka tsere zuwa cikin kasar Sudan, bayan da gwamnatin Sudan ta bude musu iyakokinta, lamarin da bakanta wa gwamnatin kasar ta Habasha.
015