Sojojin Kasa Na Iran Sun Gwada Sabon Makami Mai Linzami Mai Sarrafa Kansa Da Ke Cin Zangon Kilo Mita 300
2021-02-14 21:14:06

Sojojin Kasa
Na Iran Sun Gwada Sabon Makami Mai Linzami Mai Sarrafa Kansa Da Ke Cin Zangon
Kilo Mita 300
Kwamandan
rundunar kasa ta sojan Iran Janar Kiyomirs Haydari ne ya bayyana haka a yayin
taron tunawa da daya daga cikin shahidan soja, Shahid Namju, tare da yin ishara
da cewa; hakan yana a matsayin karawa sojojin kasar karfi ne.
Kwamandan sojojin kasa na Iran din ya kuma ce; Sabon makami mai linzamin da aka gwada yana dauke da na’urori a tattare da shi, da suke sa shi ganin inda zai kai hari da kyau, domin kare iyakokin jamhuriyar musulunci ta Iran a cikin kowane yanayi. 031
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!