Paparoma Da Zai Ziyarci Iraki, Zai Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar ‘Yan’uwantaka Ta “Yan’adamtaka Tare Da Ayatullah Sistani

2021-02-14 21:03:40
Paparoma Da Zai Ziyarci Iraki, Zai Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar ‘Yan’uwantaka Ta “Yan’adamtaka Tare Da Ayatullah Sistani

Jakadan Iraki a fadar “Vatican” Rahman al-amury ne ya bayyana cewa ziyarar ta shugaban darikar kiristanci ta Roman Katolika ta duniya, Paparoma Francis zuwa kasar ta Iraki, tana a matsayin sakon zaman lafiya ne zuwa ga duniyar musulunci.

Jakadan na Iraki a Vatican ya kara da cewa; Paparoman yana son karfafa hanyoyin tattaunawa a tsakanin addinai da kuma rayuwa a tare cikin zaman lafiya da fahimtar juna.

Har ila yau Paparoman da zai gana da Ayatullahi Sistani zai tattauna da shi akan hanyoyin fada da tsattsauran ra’ayi da ta’addanci irin na kungiyar Da’ish.

Wani sashe na bayanin jakadan Irakin a fadar “Vatican” ya kunshi cewa; Paparoman zai yi kira ga dukkanin ‘yan siyasar Irakawa da su rungumi tattaunawa domin karfafa yarda da juna a tsakaninsu. 031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!