​Pelosi: Wasu Matsoratan ‘Yan Jam’iyyar Republican Suka Ki Yarda A Hukunta Trump

2021-02-14 14:06:16
​Pelosi: Wasu Matsoratan ‘Yan Jam’iyyar Republican Suka Ki Yarda A Hukunta Trump

Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta bayyana cewa, wasu matsorata ne daga cikin ‘yan jam’iyyar Republican suka ki amincewa da a hukunta Donald Trump.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani jawabi da ta gabatar a jiya bayan wanke Trump da majalisa ta yi daga aikata laifin tunzura jama’a domin kai hari kan ginin majalisa, shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta bayyana cewa, wasu matsorata ne daga cikin ‘yan jam’iyyar Republican suka ki amincewa da daukar matakin tsige Trump.

Ta ce abin mamaki wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar Republican sun tsaya a gaban majalisa suna kiran Donald Trump mai laifi, wanda ya cancanci a hukunta shi, amma da aka zo kada kuri’ar hukunta shi kuma sai suka ja da baya.

Pelosi ta ce irin wadannan ‘yan majalisa suna tsoron kada su rasa matsayinsu ne, saboda cibiyoyin da suke tsaya musu wurin zabe da kuma abin da suke samu, wanda kuma suna tsoron rasa hakan.

Trump dai ya tsallake rijiya ta baya ne bayan da wasu sanatoci ‘yan kalilan suka ki amincewa da a hukunta shi, wanda hakan ne ya ba shi damar tsallakewa.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!