Najeriya: Cutar Corona Tana Ci Gaba Da Kara Fantsama

A cikin lokutan baya-bayan nan cutar
corona tana ci gaba da kara fantsama a sassa na tarayyar Najeriya.
A wani rahoto da jaridar Premium
Times ta buga ta bayyana cewa, tun da aka shiga shekarar 2021 Korona take ta
kara tsananta a Najeriya fiye da shekarar baya a lokacin da cutar ta bullo a
duniya.
Haka kuma mutuwa sakamakon kamuwa da
cutar ya karu matuka inda a jere a cikin kwanakin nan kullum rana sai an samu
wadanda suka rasu a dalilin kamuwa da ita.
Sakamakon gwajin cutar da hukumar
dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta fitar na wannan mako ya nuna cewa mutane
5,916 ne suka kamu da cutar sannan mutane 68 suka mutu a sanadiyyar kamuwa da
ita daga ranar Litinin zuwa jiya Asabar,
13 ga wannan Faburairu.
An yi wa mutum 1,398,630 gwajin
cutar a Najeriya, daga cikinsu kuma mutane 144,521 sun kamu, inda ya zuwa yanzu
mutum 23,921 aka killace a wurare da aka kebe ana kula da wadanda suka kamu,
sannan kuma an sallami mutum 120,399. Mutane 1,747 kuma sun mutu.
Jihohin Legas, Filato, Kaduna, Oyo,
Rivers da babban birnin tarayya Abuja, su ne suka fi yawan wadanda suka kamu da
cutar a Najeriya.
Yanzu haka dai Najeriya ta ware kudi
da suka kai naira biliyan goma, domin fara aikin samar da maganin cutar korona
a cikin gida, kamar yadda kasashe da dama suka himmatu wajen yin hakan.
015