WHO Ta Bukaci China Ta Yi Bayyani Kan Ainahin Lokacin Bullar Korona

2021-02-14 11:06:20
WHO Ta Bukaci China Ta Yi Bayyani Kan Ainahin Lokacin Bullar Korona

Hukumar Lafita ta Duniya, WHO, ta bukaci kasar China da ta yi karin haske game da rade-raden cewa annobar cutar korona ta bulla a kasar tun kafin watan Disamban 2019.

Shugaban tawagar kwararun hukumar ne da suka ziyarci kasar ta China domin gano assalin tushen cutar ne, ya bayyana hakan.

Peter Ben Embarek, ya nuna matukar bacin ransa game da rashin samun issasun bayyanai game da binciken da hukumar ta je yi birnin Wuhan.

Mista Embarek, ya ce akwai bayyanan da basu wadanda zasu taimaka gayen wajen gano asalin cutar.

A watan Disamba na shekarar 2019 ne aka bayyana bullar cutar ta korona a birnin Hubei dake tsakiyar kasra China, saidai wasu bayanai sun ce cutar ta bulla tun kafin lokacin a tsakanin watan Oktoba zuwa Disamban.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!