Chadi : Zanga zangar Adawa Da Takarar Shugaba Deby Na Yaduwa
2021-02-14 10:46:48

Jami’an tsaro a kasar Chadi, sun sake murkushe wata zanga zangar masu adawa da sake takarar shugaban kasar Idriss Deby a karo na shid
Bayanai daga kasar sun ce an cafke mutane da dama sannan wasu sun jikkata yayin zanga zangar da wasu jam’iyyun adawa da kungiyoyin farar hula na kasar suka kira a jiya Asabar.
An N’Djamena, ‘yan sanda sunyi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga zangar.
Daga bisani dai kura ta lafa a cewar rahotannin.
A kwanakin baya ne jam'iyya mai mulki a kasar ta tsayar da Shugaba Idriss Deby Itno a matsayin dan takararta a zaben da za a yi a watan Afrilu mai zuwa.
Deby, mai
shekaru 68 ya dare kan karagar mulkin Chadi ne a shekarar 1990, bayan tawayen
da ya hambarar da tsohon shugaba Hissene Habre.
024
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!