Najeriya:Masu Zanga-Zanga Sun Sake Dawowa Lekki TollGate A Birnin Lagos

2021-02-13 20:43:09
Najeriya:Masu Zanga-Zanga Sun Sake Dawowa Lekki TollGate A Birnin Lagos

Masu zanga-zanga akalla 28 ne jami’an tsaro a birnin Lagos na kudancin tarayyar Najeriya suka kama a mashigar ‘Lekki Tollgate’ a safiyar yau Asabar bayan da aka bude mashigar a karon farko tun lokacinda aka rufe ta a cikin watan Octoban shekarar da ta gabata.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa matasa da dama ne suka fito titi mai isa zuwa mashigar a safiyar yau Asabar, inda suke nuna korafinsu kan sake bude mashigar ta Lekki Tollgate tun ba’a kammala bincike kan zargin kissan wasu masu zanga-zanga a mashigar a shekarar da ta gabata.

A ranar 20 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ce dubban masu zanga-zanga suka rufe mashigar ta Lekki Tollgate saboda neman gwamnatin tarayyar Najeriya ta kawo karshen rundunar SARS ta yaki da ‘yan fashi da makami a kasar don irin ta’asar da take aikatawa kan mutanen da basu san hawa ko sauka ba.

An zargi jami’am sojojin kasar da bindige wasu masu zanga-zanga a wancan gangamin. Amma gwamnatin tarayyar kasar ta musanta zargin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!