Araqchi: Yarjejeniyar Nukiliya Ba Ta Da Amfani Ga Iran Matukar Ba A Dauke Mata Takunkumi Ba

Mataimakin ministan harkokin wajen
kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa, yarjejeniyar nukiliya da aka
cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya ba ta da wani amfani ga kasar
ta Iran, matukar ba a janye takunkuman da Amurka ta kakaba mata ba.
A wani bayaninsa ga wasu kafofin
yada labarai a yammacin jiya a birnin Tehran, Mataimakin ministan harkokin
wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada cewa, Iran ba za ta taba
komawa yin aiki da wannan yarjejeniya ba, matukar dai Amurka ba ta janye
takunkuman da Donald Trump ya kakaba mata ba.
Ya ce, idan gwamnatin Joe Biden tana son
Iran ta ci gaba da yin aiki da wannan yarjejeniyar kamar yadda aka rattaba
hannu a kanta, to dole ne ta janye wa Iran takunkuman da Trump ya kakaba mata,
sannan kuma a ga tasirin hakan a aikace, a lokacin ne Iran za ta koma yin aiki
da yarjejeniyar kamar yadda take yi a baya.
A lokacin yakin neman zabe Joe Biden
ya sha alwashin komawa cikin yarjejeniyar nukiliya da aka kulla tare da Iran ba
tare da wani sharadi ba, amma bayan lashe zabe ya gindaya sharadin cewa, dole
ne Iran ta koma yin aiki da yarjejeniyar maimakon matakin jingine yin aiki da
wasu bangarorinta da ta dauka.
Iran dai ta ce tana da hakkin daukar irin wannan mataki kamar yadda bangaren na 36 na yarjejeniyar ya ba ta damar yin hakan, matukar wata kasa daga cikin kasashen daga suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya bai yi aiki da ita ba, wanda kuma Amurka baya ga saba wa yarjejeniyar, ta fice ne daga cikinta ma baki daya.
015