Yemen: Sojojin Mamaya Na Saudiyya Sun Fara Janyewa Daga Gundumar Marib

Sojoji gami da dakarun sa-kai na
kabilun larabawan Yemen sun tilasta sojojin mamayar Saudiyya a garin Marib da ke
yammacin kasar ta Yemen ficewa daga yankin.
Tashar Almasirah ta bayar da rahoton
cewa, an ga motoci masu sulke na sojin Saudiyya suna janyewa a jiya daga wasu
yankuna da suka kafa tunga a cikin gundumar Marib a yammacin kasar Yemen.
Rahoton ya ce hakan na zuwa sakamakon
tsayin dakan da sojoji gami da dakarun sa-kai na kabilun larabawan Yemen suke
yi ne wajen fuskantar sojojin mamayar Saudiyya a garin Marib, bayan gumurzu da
karan batta na tsawon fiye da shekaru biyu da ake yi a yankin mai matukar
muhimmanci.
A cikin makon nan sojojin na Yemen
gami da dakarun sa-kai na kabilun larabawan kasar da suka hada da na kungiyar Ansarullah da aka fi sani da
Alhuthi, sun kaddamar da wasu hare-haren ramuwar gayya a kan babban filin sauka
da tashin jiragen sama na yankin Abha a kudancin Saudiyya, wanda hakan ya jawo
asarori a kan kaddarorin da ke wurin.
Baya ga haka kuma a jiya Juma’a sun
sake kai wani farmakin da jirage marassa matuki a kan babban filin sauka da
tashin jiragen sama na sarki Khalid bin Abdulazizi da ke kusa da birnin Riyad,
wanda kuma ficewar sojojin na Saudiyya daga yankin Marib na Yemen, na zuwa ne
bayan wadannan hare-hare na dakarun na Yemen.
015