An Yi Girgizar Kasa Mai Karfin Ma’aunin Ritcher 5.9 A Kasar Tajikistan
2021-02-13 09:23:26

Rahotanni daga kasar Tajikistan na
cewa, a daren jiya an yi wata girgizar kasa mai karfin ma’aunin ritcher 5.9 a kasar, amma ba tare samun asarar rayuka ba.
Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a daren jiya an ji girgizar kasa a cikin kasar
Tajikistan, wadda aka bayyana cewa ta kai ma’aunin ritcher 5.9, wanda kuma
lamarin ya auku ne a wani yanki mai tazarar kilo mita 420 a gabashin birnin
Doshambe fadar mulkin kasar, a kan iyaka da kasar China, amma duk da hakan an
ji motsin kasar a cikin birnin.
Baya ga haka kuma a cikin yankunan
arewacin kasashen India da Pakistan an ji motsin kasar a lokacin da lamarin ya
faru, sai dai babu wani bayani kan asarar rayuka.
Sai dai wasu rahotanni sun ce a
yankin Keshmir na Pakistan wasu shedun gani da ido sun bayyana cewa, wasu
bangaye sun zube sakamkon motsin kasar.
015
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!