Shugaban Kwamitin Wasannin Olympic Zai Yi Marabus
2021-02-11 20:48:15

Kafofin yadda labarai na Japan, sun rawaito cewa, shugaban kwamitin tsara wasannin Olympic da za a yi cikin watan Yuli a birnin Tokyo, Yoshiro Mori na shirin bayyana marabus dinsa daga shugabancin kwamitin a wannan juma'ar.
Wani na kusa da shi, ya ce M. Mori, zai yi marabus a ranar juma'a a lokacin wani zaman taron kwamiti.
Shi dai Yoshiro Mori, dan shekaru 83, a makon jiya a cikin wata tattaunawa ya ce mata ba su da dabbara ko fahimtar yin kammalalen jawabi a lokutan taruka, abin da ya janyo tsokaci a ciki da wajen kasar ta Japan.
Tun farko
a bara aka shirya yin gasar ta wasannin na Olympic a lokacin bazara, amma aka dage har
ya zuwa wannan shekara saboda annobar korona da ta dagula al’amura a duniya.
024
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!