Alkalin Alkalan Iran: Amurka Tana Canzawa ‘Yan Ta’adda Wuri Da Sunan Yaki Da Ta’addanci

2021-02-11 15:04:04
Alkalin Alkalan Iran: Amurka Tana Canzawa ‘Yan Ta’adda Wuri Da Sunan Yaki Da Ta’addanci

Alkalin alkalai na Jumhuriyar Musulunci ta Iran Hujjatul Islam Ibrahim Ra’esi wanda ya kammala ziyarar aiki a kasar Iraki ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka tana canzawa mayakan kungiyar Daesh a yankin wurare a dai-dai lokacinda kasashen yankin musamman Iran, Iraki da Siriya suka fafatawa da ragowar mayakan na Daesh.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ra’esi yana fadar haka ne a lokacin ganawarsa da shugaban kasar Iraqi Barham Saleh a jiya Laraba a birnin Bagdaza.

Ra’esi har’ila yau ya bukaci gwamnatin kasar Iraki ta gaggauta bincike don hukunta wadanda suke da hannu wajen kisan manya-manyan kwamandojin kasashen biyu Janar Qasim Sulaimani da kuma Mahdi Almuhandis, wadanda suka kasance jaruman yaki da kungiyar Daesh a kasashen biyu.

Janar Kasim Sulaimani dai ya na daga cikin kwamandojin sojojin kasar Iran wadanda suka taimakawa wajen kawo karshen ikon kungiyar Daesh a kasashen Siriya, Iraki da kuma Lebanon.

Amma a farkon shekarar da ta gabata gwamnatin Amurka da tashude ta kashe shi da wasu wasu abokansa na kasar Iraki a lokacinda ya isa kasar Iraki daga kasar Siriya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!